ASSALAMU ALAIKUM...Muhammad Abba Gana daga
DUNIYAN FASAHA ke muku fatan alkairi, insha Allah yau zan
koya muku yanda ake gyara kan socket na fanka, tibi, sidi kodai
wani abu makamancin haka mai amfani da wutan lantarki in ya
bachi ko ya karye ba tare da zuwa wajen mai gyara ba ko
tuntuban wani, amma a yanzu zanyi amfani da dutsen guga ne,
Abun kula!! bazamu dauki alhankin jinkata ko mutuwar wani
ba, da izinin Allah in ka bi sharruda da hanyoyin da zan
zayyano ba wani matsala da za,a samu. Wutan lantarki de kowa
yasan illarsa kuma da yanda ake amfani dashi, Abu na farko
shine ka cire tsoro a zuciyanka in har kasa tsoro a zuciyarka,
shakka, ko mumunar fata ko kuma cewa bazan iyaba ko ba
hurumina bane to bazaka taba tsinana abun kirki ba.
Abun da kake bukata wajen yin gyara:-
. Ma dauri kuma magwaji (school driver)
. Kan socket mai kai biyu
. Malika wanda akafi sani da black-tabe
Ma dauri ko magwaji (school driver) wanda aka fi sani da
tester a turance wani kayan aikin fasaha ne da masanan wutan
lantarki ko gyaran mota suke amfani dashi dan sawwake aiki,
shi wannan abun aikin sa shine daure note yayin da ake aiki,
kuma ana iya amfani dashi wajen gane ko akwai wuta a jikin
igiyar da kake aiki, ana iya samun sa wajen masu siyar da kayan
wuta, rahusar farshi ne dashi komai tsadar sa baya wuce naira
hansin 50 zuwa naira saba’in 70.
Kan socket wanda akafi sani da head plug a turane, wannan
wani dan karamin malika ne da masanan wutan lantarki suke
amfani da shi wajen canza kan soket na wuta in yasamu
matsala, socket plug din sun kasu kashi biyu akwai mai kai daya
sannan akwai mai kai biyu, ko wannen su akwai mai stada
akwai mai saukin sa amma ko wanne ka siya zaka iya amfani
dashi sai dai komai mai tsada yafi jimawa akan mai sauki kuma
ba tsada ba har zuwa can bane mai kyaun kafa biyu baya wuce
naira hamsin 50 zuwa dari 100. Mai kafa uku ne suke da dan
tsada saboda akwai wanda ake sawa a abubuwa masu jan wuta
kamar su firiji, murhun girki da dai sauransu, dan amafani da
kaya masu jan wuta sai ka siya mai stadar wanda farashinsa a
yanzu ya kai naira dari biyar 500. Amma dan sawa a yan kana
nan abubuwa wanda basu jan wuta zaka iya siya mai saukin
wanda farashin sa bazai wuce naira dari 100 zuwa dari biyu 200
ba, wasu lokutan yakan iya jimawa ya dangana ne da aikin da
ake masa.
- Malika wanda akafi sani da black-tabe shi wannan malikar
ana amfani dashine wajen lika igiyan daya bule koya dan samu
targade saboda gudun matsaloli dazai iya jawowa, amma mata
suna aiki dashi a harkokin su na yau da kullum irin su lalle, duk
abunda na irgo za,a iya samunsu a kasuwa wajen masu sayar da
kayan wuta baza,a kuma rasa a kananan shagunan mu ba.
Yanda zaka canza wanda ya samu matsala
Abu na farko da zaka farayi shine cire tsohon kai da yake jikin
round socket naka wanda ya samu matsala sai ka kunce shi da
testern ka, amma akwai wasu igiyar irin na tv koh na fanka
wanda ba,a taba canza musu kai ba wannan zayyi wuya ka iya
kunce wa, saboda ba wajen note in haka ya kasance to mafita
daya kake dashi shine yanke sama kusa da kai din wanda ba
wani mastala zai kawo ba muddin ka siya wani kai din.
Bayan ka kunce kai din ko ka yanke in kasa hankali zaka ga
igiyoyi biyu ja da kuma baki amma ba lallai bane ka samu ja da
baki zai iya zama wasu kaloline koma wani irin kala ka ci karo
dashi zayyi aiki sannan akwai wasu wanda suke zuwa da igiya
uku a ciki za,a iya samun biyun da abu a ciki dayan ba komai
zai iya zama kuma dukka su zo dashi in har haka ya kasance to
ja da baki kawai zaka dauka saboda sune masu amfani dayan
baya aikin komai ana sasane in daya daga cikin biyunnan ya
samu matsala sai a maye gurbinsa.
Abu na biyu shine stefe kan igiyar saboda samun damar shiga
cikin sauki, sannan zaka yanke dayan da bazakayi aiki dasi ba,
zaka samu rezan ka ko kuma wuta wanda zaka dan kona yayi
saukin fita akwai wani kuskuren da mutane suke yi shine tsefe
igiyar wuta da baki ko wani igiya makamancin haka, yin hakan
babban illane saboda duk wani abunda aka kera ana sarrafasa
ne da wasu sinadari wanda ni ko kai ba lallai bane musan su ba
balle kuma musan menene aikinsa saboda haka yana da kyau
mu daina amfani da bakin mu wajen biyan wani yar karamar
matsala dan zai iya haifar da illa babba bangaren lafiyarmu.
Abu na uku shine bude kan socket da ka siyo, zakayi amfani da
madaurinka wato tester koh schooldriver a turance, wajen bude
note dake daure a jikin kan wanda zai baka damar sa igiyoyin,
bayan ka bude marfin zai rabu kashi biyu daya ta bangaren nan
dayan kuma ta can hakan ba wani matsala bane zai koma daidai
kamar yanda yake a da. Bayan ka bude marfin wannan
mazaunin mai dauke da kafafuwan da suke shiga cikin socket
din zaka ga wasu notuna guda biyu wanda aikin su shine rike
igiyoyin da za,a cusa cikinta wanda kowanne da zaman sa da
kuma aikin sa, notunan wasu suna zuwa a bude wasu kuma suna
zuwa ne a daure in ya kasance a daure sai ka dauki madaurinka
ka bude wannan notunan guda biyu yanda igiyar zata samu
damar shiga tsakiyar ba tare da wani gardama ba.
Abu na hudu sai ka dauki igiyar naka na fanka ko tv wanda ka
tsefe bakin sa sai ka tura na faro cikin rami daya, zaka iya sa ko
wani kala a ramin farko saboda basu da takamammen wajen
zama duk wanda ya samu zai yi aikin sane amma abun kula
anan shine kada ka yarda koda itsinin gashin dayan igiyar ya
hadu da dayan wajen sawa saboda zai iya kawo babban hatsari,
ka zuba hankali sosai ka tabbatar da cewa ko wanni gida yana
zaune da dan gidansa, bayan ka sa ka tabbatar daya shiga sai ka
daure note dake rike sa sosai sannan ka sa dayan kabi da’idan
da ka dayan wajen sawa shima sai ka daure sa sosai, ka dan ja
kasan saboda tabbatar da cewa sun shiga sosai in ka ja sai wani
ya fito to ka kunche note nasa kasake cusasa sosai yanda note
din zai kamasa sosai.
Abu na biyar shine mayar da murafan da suke cire kafafuwan
zaka fara sa daya in ya zauna daidai sannan ka saka dayan in su
hau cibcib sai ka dauki note da ka fara kuncewa sai ka mayar
tare da dauresa da madauri sosai ka tabbatar ya dauru daidai
sannan kada ka daure sa can yanda zai iya fashewa saboda
bashi da karfin da zai jure dauryiya sosai. Wasu igiyoyin suna
da kauri sosai zayyu ka gama daurewa kasan bai kamu sosai ba
sai ka dauki malikanka wato black-tabe sai ka matse kasan sosai
sannan ka daure sa da mallinkan shikenan ka gama.
Abu na karshe shine gwadawa in babu wuta sai ka jira a kawo in
kuma akwai sai ka je ka saka sa da izinin Allah zayyi,
Abun kula!!
- Ka tabbatar igiyoyin da suke ciki guda biyu basu hadu da
junansu ba
2- Ka tabba a jikin gaba daya igiyar ba inda ya bare ya hadu
da junanasa, yin daya daga cikin wayannan zai iya kai mutun
zuwa ga jinkata ko kuma mutuwa wanda muke fatan hakan
bazai faru ba.
Bazamu dauki alhankin jinkatar ko mutuwar wani ba
in baka/ki fahimti wanana mujallar sosai ba zaka/ki iya
ganin video kai tsaye ta hanyan ganin wannan videon
watch full toturial here
UNDER MAINTENANCE
Gud