Polaroid
HAUSA TECH | KOYON HADA WEP


   

Shin kana son ka tuntube mu:-
aika da sakon txt msg zuwa @+2348140465722

Share Button
kasa

SITE-SEARCH

LATEST UPDATES

Raliya page 9 na shafi'u dauda giwa

Raliya page 9 na shafi'u dauda giwa
RALIYA Littafin Shafi"u dauda giwa Typing:- sadeeq shehu shariff Post:- Shuraih Usman @shuraih 99% Page 9 . AYARIN 'yan sandan da suka kamo jarmai suka ci birki a daidai ofishin A-C-P AMINU JANGWARZO" tsayawarsu keda wuya suka fito da shi" nannade da ankwa a hannayenshi tare da murgujejen akwatin kudin" Dan sandan da yake dauke da akwatin sun shashi a tsakiya rike da bindigogi" domin kuwa suna fargavar wata kila yana da layar bata" . . Da shigarsu ofishin JANGWARXO suka sameshi tare da A-C-P ßilya" 'yan sandan suka sara ma tsofaffin sannan babban cikinsu yace-: "An gama aiki yallabai gashi nan mun kamoshi a motar haya xai gudu xuwa wani kauye" ga akwatin da ya sato" A-C-P JANGWARXO yayi saurin amshe akwatin a hannunsu" sannan ya daka masu tsawa yace" "ku daukeshi ku kaishi gidan tuhuma ku kulleshi" kada a bari wani ya kusanci inda yake har xuwa nan da lokacin da xan baku umarni nan gaba" . . 'yan sandan suka cakumi jarmai wanda bakinshi ya karkace ya koma gepe daya" yana ta xubar da jini" kamar gilmawar walkiya" nan da nan har sunyi ciki dashi sun bace" tsofaffin 'yan sandan biyu suka kalli juna cikin tsananin murna" sannan suka fice da sauri domin su kaiwa kwamishina ya bude ya basu nasu kason" Cikin minti uku har sun garxaya a mota sun sami DANMASANI" yana ta kai da kawowa a wani kebantaccen gida na sirri da ya ce su sameshi acan idan sun amso akwatin kudin" Yana a tsaya yana kallonsu suka tunkareshi da akwatin suna fara.a ganin haka saiya shiga cikin wani daki na sirri" tsofaffin 'yan sandan suka bishi" ciki suka sameshi har ya xauna akan kujera ya dora hannuwanshi akan teburin dake a gaban kujerar fara.a akan fuskarshi da kuma murnar ganinsu" . . "me kuka tsaya jira tun daxun ina xama jiranku?" DAN MASANI" ya tambauesu yana shapa bindigarshi dake a boye a kugunshi domin ya tabbatar tana nan" sai jangwarxo yace-: "mun sami matsala ne a wurin nemanshi" domin kuwa da farko tashar jirgin sama da kuma na kasa muka tura yara su nemoshi" sai daga baya muka sami cikakken bayanin an ganshi ya hau wata mota ta haya da akwatin xai nufi wani kauye ya boye acan" kafin yara subi motar yayi nisa" amma an samu sa.a sunxo mana dashi yana can gidan tuhuma munce su boyeshi sai sunji daga garemu" Ga akwatin kudin munxo dashi" . . Suka ajiye akwatin a gaban kwamishina Dan masani" sannan suka bushe a tsaye suna jiran umarni daga wurinshi" da farko yaso nan take ya ciro bindigar ya gama dasu" to amma kuma saiya canxa shawara" ya kamata ya bude akwatin domin ya dauke hankalinsu" idan suka mayar da hankalinsu wajen kallon kudin sai ya harbesu a tsanake" . . DAN MASANI" ya ciro wani siririn mabudi a aljihunshi ya saka a cikin kwadon akwatin ya dade yana mirxawa" xuwa can sai kwadon ya bude" kwamishina yayi murmushin farin ciki tun kafin yasa hannu ya bude murfin yaga abinda yake ciki" ya dubi 'yan sandan dake a tsaye a gabanshi suna ta xufaa" yace dasu" "to ina fatan dai kowa a cikinku ya gama tunanin abubuwan da xaiyi da wadannan kudi" domin kuwa da xarar mun kammala rabasu" xamuyi ritaya" sai kowa ya nemi kwakkwaran kasuwanci ya para" nidai dama na gama nawa tunanin kasar ingila xan koma da xama" ban sani ba ko kuma kun kammala taku shawarar" . . A-C-P ßILYA yace dashi" "mu dukanmu yallabai mun gama shirya inda xamu nufa" samun kudin dama ai yafi sarrafasu wahala" suka tuntsire da dariya a lokaci guda" kwamishina Danmasani yayi dariyar mugunta" sannan ya bude murfin akwatin" manyan 'yan sandan uku suka ja da baya a tsorace cikin tsananin rudani" a yayin da suka ci karo da abinda ke cunkushe a cikin akwatin" wasu jibgin kaya ne an kimshesu suna ta faman tsami" da kuma littafan karatu da takalma" a kusa da wani kallabi wani katin shaida ne na jami.a wanda ke dauke da hoton kyakkyawar budurwa tana ta fara.a a gepen hoton an rubuta sunanta da mayan bakake" #RALIYA_A_MUNTARI . =======>*****^*****<====== : NAZIRU ya farfado daga suman tsayen" yayi sauri ya rupe murfin akwatin domin kada wani yaxo wucewa ya hango makudan kudin dake a ciki" SHEGEN SAMA yayi ajiyar xuciya ya tambaya" "A ina ka samo wannan akwatin naziru?" A ina ka samo wadannan kudi haka...?" Naziru ya daga kai ya dubeshi cikin tsananin firgici yace dashi" "Wallahi nima wurin RALIYA kanwata na amsoshi ita ta bani da hannunta tace inxo in bude mata" ina kyautata xaton ita kanta bata san abinda ke cikin akwatin ba" . . SHEGEN SAMA yayi murmushin farin ciki yace wa Naziru" "Allah ne ya bamu wannan makudan kudi Naziru" domin kuwa babu wanda yasan daga ina suke" Abinda yafi kawai shine mu rabasu ni da kai kowa ya gudu yabar garin" muje can wata duniya mu boye ba wanda zai sake jin labarinmu har abada" . . NAZIRU ya harareshi sannan yace-: "Vaka da hankali SHEGEN SAMA" kana tsammanin akwai rabonka a cikin wadannan kudin?" to wannan kudi nawa ne ni da kanwata" sai naga dama in dauko wani abu a ciki in dan tsakura maka domin kuwa ka riga ka gani" . . SHEGEN SAMA ya hade fuska yace da Naziru-: "Kai ma kasan cewar wannan baxae taba yiwuwa ba" dole ne mu raba wannan kudin mu biyu" . In ba haka ba daga nan..... SHEGEN SAMA" ya hade fuska yace da Naziru" "kai ma kasan cewar wannan bazai taba yiwuwa ba" dole ne mu raba wannan kudin mu biyu" in ba haka ba daga nan xan hau keke inje in sanarwa 'yan sanda acan gari suxo su amshi kudin da hannunsu" Naziru ya kurawa shegen sama idanu cikin tsananin kulewa" ya dade da sanin halinshi na rashin sabo" akan dan abu kankani zai iya yiwa koda uwarshi rashin mutunci ne" kuma Naziru ya tabbatar idan har bai yarda sun raba kudin ba" to ko shakka babu shima yayi asararsu" domin kuwa kai tsaye shegen sama xai wuce xuwa wurin 'yan sanda" . . NAZIRU yace dashi-: "to naji xamu raba kudin" amma uku xamu raba duk da kanwata RALIYA kowa ya dauki kaso dai- dai" SHEGEN SAMA ya sake murtuke fuskarshi" duk yayi sharkaf da xupa kamar kuturu yace da Naziru" "Baxan taba amincewa ka ha'inceni ba Naziru" domin kuwa ba yau ka fara yi min irin wannan hadamar ba" kudi mu biyu muka tsince su ni da kai" kuma mu biyu xamu rabasu" idan baka amince ba" sai dai kowa ya hankura akaiwa 'yan sanda su raba" . . NAZIRU ya kidime yana durkushe ya dafa akwatin kudin da hannunshi" hakika shegen sama ba abokin amana bane" domin kuwa irin wannan ta taba faruwa a tsakaninsu" a lokacin da suka shiga gidan fulani dake a bayan gari suka sato agwagi biyar suka xuba a cikin buhu" Naziru ya barwa shegen sama agwagin kafin jama.a su tafi gona su tafi dasu gari su sayar a kasuwa" Lokacin da Naziru ya biyo ta gidansu shegen sama" tuni har yakai gari ya sayar da agwagin" haka sukayi ta rigima akan kudin har yanxu bai gama biyanshi nashi kason ba" Don haka a wannan karon Naziru yasan cewar koda ace amincewa yayi su raba kudin biyu da shegen sama" dole ne saiya ha'inceshi" saboda tsabar hadama" don haka ya xama dole yayi kokari yayi maganin shegen sama" a wannan karon" . . NAZIRU yace dashi-: "Naji na amince xamu raba kudin mu biyu" to amma baxae yiwu mu raba wadannan kudin yanxu ba" saidai mu boye su xuwa nan da kwana biyu idan babu wani abu da ya faru" saimu ciro abinmu sun xama namu" shegen sama ya xaro idanu cikin rashin yarda" yace da Naziru" "A ina xamu boye wadannan makudan kudi?" Naziru yace-: "muje can fadamarmu mana mu boye su" mu gina rami mu binne akwatin bayan komai ya lafa saimu tono abinmu mu raba" . . SHEGEN SAMA" yayi shiru cikin xargi" xuwa can yace" "xan aminci muyi hakan" amma kai ma ka amince idan muka binne wadannan kudin to baxan yarda ka matsa daga inda nake ba" sai dai ka dawo nan dakina mu rika kwana tare" ko bayi xaka shiga sai dai mu shiga tare" domin nasan ha.incinka NAZIRU so kake yi ka ha"inceni ban yarda dakai ba" Naziru yace dashi-: "Na amince" xomu tafi bakin rafi mu binne akwatin nan shegen sama" domin kuwa idan tsautsayi ya ratsa sai kaga wani shegen ya karu mun xama mu uku" shekiyan samarin biyu suka fito daga cikin xauren NAZIRU yana rungume da akwatin a hannunshi" shegen sama yana binshi a baya" suna tafiya xugum-xugum sai kace xauje jana.ida" bayan sunje bakin fadamar ne" inda ke cunkushe da shuke shuke" dangin kabewa da kuma tumatir" wani bangaren kuma gonakin rake ne da kuma kubewa 'yar damina" Naziru ya nuna gindin wata bishiyar dorawa dake a saman tudu kafin a gangara cikin fadamun a nufi bakin rafi" . . "A gindin bishiyar can ya kamata mu boye kudin nan" ya cewa shegen sama yana nan cikin xargi ko fara.a baya yi" ya girgixa kai bai cewa Naziru komai ba" yana ta kaffa-kaffa dashi domin kada ya tsere da akwatin yabar shi" xuwa can sai suka samo magirbi a cikin fadamar tumatirin wadanda masu aiki suke ajiyewa kafin su dawo washegari" Naziru ya mikawa shegen sama daya ya ajiye akwatin a gepe daya" shima ya dauki magirni daya" nan da nan suka dara gina rami sam! Sam!! Kamar suna gina kabari" bayan sunyi nisa da aiki" ramin yayi fadi sai suka dawo suna haka cikin ramin daya bayan daya" idan wanna ya gina ya gaji" sai ya fito ya barka dayan shima ya gina" a haka har suka kammala gina dogon ramin" Naziru ya dauki akwatin ya saka a ciki yabar shi a tsaye" suka sa hannu suka tura kasar ta cike ramin" sannu a hankali suka rufe saman akwatin suka haye saman ramin suna tattakawa domin wurin ya saje da sauran kasar fadamar" . . Bayan sun kammala ne sai Naziru ya kwashe magirban ya rike daya a kowanne hannunshi" ya daga kanshi sama a tsorace ya cewa shegen sama" "waccan jirgin menene" shegen sama" anya kuwa bamu suka biyo ba?" Shegen sama ya daga kanshi a tsorace ya kalli sama" yana kokarin ganin jirgin da Naziru ke nuna mashi" ba xato da tsammani sai yaji wani abu mai kama da guduma ya tsaga mashi kokon kai tas!! . . Shegen sama yayi kururuwa sannan ya xube a kasa yana kokarin ya dafe kanshi ne" sai naziru ya sake daga magirbin ya dankara mashi a kokon kai" kan shegen sama ya sake tarwatsewa" idanuwanshi suka kakkafe............
Back to posts
This post has no comments - be the first one!

UNDER MAINTENANCE
Recent Wapmaster services
< >wap din talla
< >hits counter
< >css style collection
< >colour code
< >code din talla
< >background color
12»
Recent Online services
< >online login
< >love calculator
< >functions.php
< >facebook login
< >date calculation
< >creat logo
12»
SHAFUKA [PAGES]
imagekuna iya samun html code,na xtgem,wapka,wordpress,e.t.c Da css,php,twig files
imageZaka iya dauko pdf ebook na mu anan kama daga kan littatafai da kuma tutorials
imageZaka iya dauko txt ebook na mu anan kama daga kan littatafai da kuma tutorials
imageZaka iya dauko DOC ebook na mu anan kama daga kan littatafai da kuma tutorials
imageGame da wannan shafin, kusan abubuwa da dama game da mu da kuma manufarmu
imageGame da ni, shiga nan kaga abubuwa da dama a game dani
imagedokokinmu, shiga nan kaga dokokin wannan shafi
imageTallata hajarka ko wacce irice ,awannan shafi mai Albarka
imagetuntubemu,shiga nan kaga yadda zaku tuntubemu
imageaika da sako, ko korafi ko tambaya game da mu ko wani abun da baka gane ba
imageku tattattauna da abokai sannan ku hadu da saBbin mutane
imagehausa tutor, sabbin fasahai, na internet
imagewasannin kan layi, na kimiya da fasaha
Shafukan Abokan hulda :
partner site
» Hausaebook.cf ()
» Keffians News teller ()
» islamic site ()
» Hausabooks ()
» Nasarawa silver stars ()
» HAUSAEBOOKS ()
» Kingsarawee fresh Music ()

SUB MENU
View
View
View
View
View
View
View

Hausa Tech statistics

Online : 1 user
today : 6 user
this week : 6 user
34 user
Total all : 11008 Visitor
visitors today visitors yesterday visitors total visitors online Reliable Counter
Reliable Counter blog counter
blog counter
SpeedCounter.net - Free web counter
Shafukan mu
Game da mu